Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC a ranar Talata sun kama wasu ma’aikatan h Bureau De Change a babbar kasuwar Wuse Zone 4.
‘Yan sandan sun fara kai samame akai-akai domin tsaftace kasuwar.
Daya daga cikin ‘yan kasuwar da ya nemi a sakaya sunansa saboda fargabar ramuwar gayya, ya ce ‘yan kasuwar sun yi hakan ne kawai saboda bacin rai domin kamen da ake yi ya zama ruwan dare da kuma karbar kudi daga hannunsu.
Wani dan kasuwa da ya tabbatar da faruwar lamarin ya yi gargadin cewa ci gaba da kai farmakin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi na iya haifar da kashe-kashe.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC dai ta sake kai samame ne a yunkurinta na daidaita darajar Naira amma duk da wannan kokarin, Naira na ci gaba da faduwa cikin sauki.