ECOWAS ta umarci jami’anta su fice daga Guinea-Bissau

Ƙungiyar ECOWAS, ta ce tawagar da ta aika ƙasar Guinea-Bissau domin ta taimaka wajen warware taƙaddamar zaɓe ta bar ƙasar bayan da shugaban ƙasar ya yi barazanar korar tawagar.

Ƴan jam’iyyun hammaya na na siyasar ƙasar dai sun dage cewa ya kamata wa’adin Shugaba Umaro Sissoco Embalo ya ƙare a makon da ya gabata.

Sai dai ya dage kai da fata cewa ba za a yi zaɓe ba sai watan Nuwamban da ke tafe.

Comments (0)
Add Comment