ECOWAS ta bukaci masu zanga-zanga a Najeriya su sauarari jawabin da Bola Tinubu yayi musu

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afurka ECOWAS ta bukaci masu zanga-zangar kawo karshen rashin kyakkyawan jagoranci #EndBadGovernance da su sauarari kiran tattaunawa da shugabankasa Bola Ahmad Tinubu yayi musu.

Cikin wata sanartwa ajiya Litinin, ECOWAS ta nuna damuwarta kan rahotannin rikice-rikice da rashe-rashen rayuka da kuma barnar dukiyoyi da aka samu yayin zanga-zanagar

Kungiyar ta bayyana cewa tana sane da yancin yankasa na yin zanga-zangar lumana kamar yanda yake kunshe kundin Dimokaradiyya da Jagoranci na gari da dokar ECOWAS ta 2001, daidai da kundin tsarin mulkin kasarnan na 1999. A ranar Lahadi, shugaba Tinubu yayi jawabi ga fusatattun matasan dake zanga-zangar da ta faro daga ranar 1 ga watan da muke ciki yana mai kiransu da su rungumi hanyar tattaunawa  maimakon zanga-zangar.

Comments (0)
Add Comment