Dubu 5 Kacal Na Mora Daga Kwangilar Kashe Mutane 7- Dan Ta’adda

Biyo bayan kama shi da rundunar yansandan jihar Zamfara su ka yi, dan bindigar da ake zargi, Abubakar Namalika, mai shekaru 30 a duniya, wanda ya shaidawa yansanda cewa yana daga cikin wadanda suka kashe wani likita mai suna Okpara Enoch na Asibitin Tarayya dake Gusau, yace naira dubu 5 kacal aka bashi domin kisan mutane 7, ciki har da marigayin likitan.

Wanda ake zargin ya sanar da haka lokacin da yake amsa tambayoyin yan jarida lokacin da kwamishinan yansandan jihar Zamfara ya gabatar da shi a helkwatar rundunar dake Gusa a jiya.

A cewarsa, wani shugabansu mai suna Shehu Bagewaye, shi yake aikensu su sato mutane amma yake biyansu kudi kalilan bayan ya karbi diyya.

Sai dai, kwamishinan na yansanda Usman Nagogo, yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma yana bawa yansanda bayanai masu muhimmanci dangane da maboyarsu, inda ya kara da cewa nan bada dadewa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan an kammala bincike.

BanditsSecurity
Comments (0)
Add Comment