Donald Trump zai ƙara haraji kan kayan Tarayyar Turai

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ko shakka babu zai ƙara haraji kan kayan da ake ƙirawa ake shiga da su Amurka daga Tarayyar Turai.

Mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa zai sanya harajin nan ba da jimawa ba, ya kuma zargi kungiyar da cin gajiyar Amurka, yana mai bayyana hakan a matsayin zalunci.

”Ba su sayen motocinmu da amfanin gonarmu, kusan babu wani abu da suke saya daga wajenmu, amma mu kusan komai daga wajensu muke saye” in ji shi.

A yau Litinin ne ya kamata shugaba Trump ya tattauna da shugabannin ƙasashen Canada da Mexico bayan sanya wa ƙasashen biyu masu maƙwaftaka da Amurka haraji da kuma China.

Tun da farko dai Trump ya gargaɗi Amurkawa cewa matakin nasa zai iya haifar da raɗaɗi, sai dai ya ce nan gaba hakan zai zama alheri ga Amurka.

– BBC Hausa

Comments (0)
Add Comment