Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen baya-bayan nan da aka samu a jihar Benue.
Rahotonni sun ce an kashe gwamman mutane a ƙauyen Umogidi da ke ƙaramar hukumar Otukpo
A wata sanarawa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce za a yi duk mai yiyuwa wajen kawo ƙarhen tashe-tashen hankula a ƙasar.
Shugaban ƙasar ya yi Allah-wadai kan amfani da abin da ya kira ta’addanci wajen rura wutar faɗan ƙabilanci a ƙasar.
Ya kuma bayar da umarnin zaƙulo maharan domin fuskantar hukunci kan laifin da suka aikata, bayan ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon harin.
A ranar Larabar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga da suka kai hari kauyen Umogidi inda suka kashe akalla mutane 46, lokacin da suka mamaye yankin.
Kisan dai ya zo ne sa’o’i 24 bayan kauyen na ‘yan kabilar Idoma ya fuskanci wani harin ‘yan bindiga da yayi sanadin rayukan mutane 3.
Har ila yau, a ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga sun kai hari sansanin ‘yan gudun hijira da ke Agan a karamar hukumar Makurdi ta jihar Benue harin da ya kashe mutane da dama.