Davido ya goge faifan bidiyon wakar Logos Olori, bayan ya fuskanci tsangwama a yanar gizo

Tauraron mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya goge faifan bidiyon waka mai cike da ce-ce-ku-ce na takwaransa, Logos Olori, bayan ya fuskanci tsangwama a yanar gizo.

A ranar Asabar, Davido ya fuskanci suka daga Musulmai da yawa a shafukan sada zumunta saboda ya yada wani faifan bidiyo na wata waka mai tsawon dakiku 45 a shafin Twitter.

Bidiyon da masu sharhi musulmi da dama suka bayyana a matsayin abin ban haushi, ya nuna gungun mazaje da suka yi ado, kuma ga alama a cikin wani taron addu’o’in musulmi ya koma rawa da waka.

Sun zargi mawakin da rashin mutunta addinin Musulunci ta hanyar hada ibadarsu da waka da raye-raye tare da yin kira gare shi da ya goge faifan bidiyon tare da ba da hakuri.

Fitattun ‘yan Najeriya irin su Ali Nuhu sun yi ta tofa albarkacin bakinsu kan hakan.

Sai dai kuma, yayin da mawakin ya yi shiru kan lamarin, bai kuma bayar da uzuri ba, kwana biyu bayan matsa masa lambaDavido ya goge bidiyon. Sawaba Radio ta tabbatar da gogewar a safiyar yau ta hanyar dubawa a shafukan sada zumunta na Davido.

Comments (0)
Add Comment