Dauda Biu ya bayar da umarnin a damke direban wata tsohuwar mota mai lalatattun tayoyi uku

Shugaban hukumar kare afkuwar hadura ta kasa Dauda Biu, ya bayar da umarnin dakile duk wasu tsofaffin ababen hawa da wadanda ba a yadda da amincin su ba fadin kasar nan.

Biu ya ba da umarnin ne a cikin wata sanarwa da jami’in wayar da kan al’umma na hukumar ACM Bisi Kazeem, ya fitar jiya a Abuja.

Shugaban hukumar ya ce umarnin ya zama dole sakamakon ganin wani faifan bidiyo na wata tsohuwar mota dauke da tayoyi uku da suka lalace a kan babbar hanyar garin Sagamu ta jihar Ogun.

Dauda Biu ya bayar da umarnin a damke motar nan take tare da mai motar, inda yace hakan ka iya jefa rayuka da dukiyoyin al’umma cikin hadari. A cewarsa, hankalin hukumar ya karkata ne ga faifan bidiyon tsohuwar motar da ke da matsalar inji wacce ke tafiya a kan babbar hanyar.

Comments (0)
Add Comment