Kwamishinan Ilmi matakin farko na jihar Jigawa , Dr Lawan Yunusa Danzomo ya bukaci daraktoci da maaikatan maaikatarsa dasu kara kokari wajen gudanar da aiyukansu domin cigaban ilmi
Dr Lawan Yunusa Danzomo yayi wannan kiran a lokacin taro da Daraktoci da kuma mataimakan daraktoci na maaikatar
Yace a matsayin sabuwar maaikatar Ilmi matakin farko da wannan gwamnati ta kirkiro akwai bukatar kara jajircewa domin marawa kudirin gwamnati baya na cimma manufarta na cigaban ilmi
Dr Lawan Yunusa Danzomo ya shawarci maaikatan dasu yi aiki tare domin cigaban ilmi matakin farko a jihar nan
Yace kofarsa a bude take wajen karbar duk wata shawara da zata kawo cigaban ilimi a jihar nan
A jawabinsa babban sakataren maaikatar , Alhaji Isiyaku S. Shehu ya bukaci maaikatan dasu mara baya ga kwamishinan domin samun saukin gudanar da aiyukansa
A jawabansu daban daban Daraktocin maaikatar sun yabawa kwamishinan bisa jagoranci na kwarai da yake gudanarwa a maaikatar