Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ta ce dan takararta Atiku Abubakar, yana da hazaka, sannan yana cikin koshin lafiya.
Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP Dino Melaye, ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya tafi kasar Birtaniya ne bisa gayyatar da gwamnatin kasar ta yi masa.
An samu rahotannin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba shi da lafiya kuma an dauke shi zuwa kasar Burtaniya domin yi masa magani.
A wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta a jiya Lahadi, Melaye ya bayyana rahotannin a matsayin na karya.
A wani rubutu na dabam a shafin Twitter, mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yada labarai Paul Ibe, ya ce ana sa ran Atiku zai gudanar da taron ne a ranakun Talata da Laraba.