Dan majalisa mai wakiltar Faskari, Kankara da Sabuwa a majalisar wakilai ta kasa Shehu Dalhatu Tafoki, ya koka da cewa hare-haren ‘yan bindiga da ake kai wa jama’ar mazabar sa ya zama abin da ba za a iya jurewa ba.
Da yake zantawa da wakilinmu ta wayar tarho, Tafoki ya bayyana rashin tsaro a mazabar sa a matsayin abin ban tsoro, ya kuma kara da cewa hare-haren da ake kaiwa Kankara da wasu sassan kananan hukumomin Faskari na jihar Katsina na kara ta’azzara.
Ya koka da hasarar rayuka da barnata dukiya da kuma kauracewar mazauna yankin sakamakon hare-haren da ake kai wa a kai a kai, inda ya jaddada babban tasirin da lamarin wajen tarwatsewar al’ummar yankin.
Da yake yaba wa kokarin gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda na magance matalar, Tafoki ya bukaci masu ruwa da tsaki ciki har da hukumomin tsaron kasa da su baiwa ‘kare rayukan yan Najeriya fifiko.
Ya bayar da misalai daban-daban na hare-haren baya-bayan nan da aka samu a mazabar, ciki har da na bakin da suka halarci wani daurin aure, inda ya ce masu garkuwa da mutane sun nemi fiye da Naira miliyan 200 a matsayin kudin fansar mutanen.