Kwamitin duban wata na kasa a karkashin majalisar koli ta harkokin addinin Islama a Najeriya yace ba a samu rahoton ganin sabon watan Muharram ba, na shekarar 1442 bayan hijrah.
Hakan na nufin cewa yau, Alhamis ita ce ranar talatin ga watan Dhul-Hijjah, shekara ta 1442 bayan hijrah, yayin da gobe Juma’a zata zamo daya ga watan Muharamm, a sabuwar shekarar musulunci ta 1442 bayan hijrah.
- Obasanjo ba shugaban da za a yi koyi da shi bane – Gwamnatin Tarayya
- Aƙalla ‘yan ƙasar Nijar 300 ne ake zargin hukumomin Libiya sun tsare
- Mutum 7 sun mutu yayin zanga-zangar bayan zaɓe a Mozambique
- Da yiwuwar Amurka ta fitar da hannunta daga yaƙe-yaƙen ƙasashen ƙetare
- Ƙungiyar dillalan man fetur ta cimma matsaya da Dangote kan sayen man fetur
Wani mamba a kwamitin na duban watan na kasa, Sheikh Salihu Muhammad Yakubu, ya shaidawa manema labarai hakan, jiya da dare.
An bayar da rahoton cewa Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto, kuma shugaban kwamitin shura kan harkokin addini a majalisar mai alfarma sarkin musulmi a Sokoto, cikin wata sanarwa a ranar Litinin, yace jiya Laraba ce ranar da za a fara duban sabon watan Muharram, shekara ta 1442 Bayan Hijrah.