Dalilan da yasa aka dakatar da shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus

Babbar Jam’iyar Adawa ta Kasa wato PDP ta sake shiga cikin rudani, biyo bayan dakatarwar da wata babbar Kotu wanda take zamanta a jihar Rivers ta yiwa Shugaban Jam’iyar na Kasa Prince Uche Secondus daga kiran kansa a matsayin shugaban Jam’iyar.

Manema Labarai sun rawaito cewa Mista Secondus yana son ya kammala wa’adin sa wanda zai kare a karshen shekarar nan.

Amma da yake yanke hukunci Alkalin Kotun Mai Shari’a O Gbasam, ya umarci Prince Secondus, ya dakatar da kiran kansa a matsayin shugaban Jam’iyar biyo bayan bukatar hakan da wasu kusoshin Jam’iyar suka yi a gaban Kotu.

Kusoshin Jam’iyar da suka shigar da karar domin dakatar da shugaban sun hada da Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da kuma Umezirike Onucha.

Alkalin Kotun kuma ya dakatar da Prince Uche Secondus, daga shirya tarukan a matakin Mazabu ko kananan hukumomi, har sai Kotun ta kammala sauraron karar.

Amma da yake jawabi kan dakatarwar Mista Secondus ta bakin mai magana da yawunsa Mista Ike Abonyi, ya ce dagataccen Shugaban Jam’iyar zai kare kansa.

Kazalika, ya ce PDP da Uche Secondus, basa tsoron zuwa gaban Kotu, inda ya kara da cewa Jam’iyar su mallakin yan Najeriya ce kuma tafi karfin wasu tsirarin mutane ciki harda masu shigar da karar.

Comments (0)
Add Comment