Rundunar yansandan jihar kano tace, kawo yanzu ta tantance masu neman shiga aikin kurtun dan sanda dubu 13 da 40 kwanaki 11 bayan tafara aikin tantancewar a jihar kano.
Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar ta kano DSP Abdullahi Haruna,shine ya bayyana hakan yayin gudaanar da aikin tantancewar a jiya juma,a a birnin kano.
DSP Haruna,ya kara da cewa wadanda aka tantance din sun fito ne daga kananan hukumomi 40 daga cikin 44 dake fadin jihar ta kano.
A cewar DSP Abdullahi Haruna, mutune 1,475 sunfito ne daga kananan hukumomin Takai, Tarauni, Tofa and Tsanywa wadanda aka tantance su a ranar alhamis din data gabata.
Sannna ya kara da cewa a ranar jum,aa,a mai zuwa zasu kammala gudanar aikin tantancewar a fadin jhar ta kano.
A cewar sa mutanen da suka rasa shiga aikin aikin tantancewar a kananan hukumomin Tudun Wada, Warawa, Wudil and Ungogo, nan gaba bada dadewa ba, za,a sanar da su ranar da zasu zo domin a tantance su.
- Gwamnatin Kano ta raba kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar
- Tinubu ya amince da kirkirar sabbin jami’o’I guda biyu
- NNPP za ta kayar da APC da PDP a zaɓen 2027 – Kwankwaso
- Dole ƴanjarida da jami’an tsaro su haɗa kai domin daƙile matsalar tsaro – Rundunar tsaro
- Ana bikin ƙaddamar da littafin tarihin Ibrahim Babangida
Sannan ya kara da cewa suna gudanar da aikin tantancewar ne cikin matakan kariya daga cutar corona kamar yanda aka umarce su.