Cutar Sankarau Ta Kashe Mutane 52 a Nigeria

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC), ta ce mutane 52 ne cutar sankarau ta kashe a jihohi 21 na kasar tsakanin shekarar 2022 zuwa ranar 5 ga watan Maris na 2023.

Rahoton halin da ake ciki da aka fitar a jiya ya bayyana cewa ya zuwa ranar 5 ga watan Maris, an samu rahoton mutane 628 da suka kamu da cutar, ciki har da mutane 52 da suka mutu a jihohi 21 a kakar cutar sankarau ta shekarar 2022 zuwa 2023.

A cewar rahoton, jihohin Abia, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Ebonyi, Gombe, Imo, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Neja, Oyo, Plateau, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara sun kasance daga cikin jihohin da aka samu rahoton bullar cutar sankarau a shekarar 2022 zuwa 2023.

Rahoton ya bayyana cewa kashi 91 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga jihohi hudu na Jigawa mai mutane 509, Bauchi mai mutane 23, Zamfara mai mutane 22 sai Oyo mai mutane 14. Rahoton yace daga cikin wadanda suka kamu, kashi 62 cikin 100 maza ne yayin da kashi 38 kuma mata ne.

Comments (0)
Add Comment