Cutar Lassa ta kashe mutum 70 cikin wata guda a Najeriya – NCDC

Hukumar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya, NCDC ta ce cutar zazzaɓin Lassa ta kashe mutum 70 a farkon wannan shekarar.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce mutum 1,552 ne ake sa ran sun kamu da cutar, yayin da ta tabbatar da kamuwar mutum 358.

Sanarwar da hukumar ta fitar wanda ta kammala haɗawa a ranar 2 ga watan Fabrairun da muke ciki, ya nuna cewa zuwa ranar haɗa rahoton, jihohi 10 aka tabbatar da ɓullar cutar a faɗin ƙananan hukumomi 58.

Jihohin da aka fi samun mace-macen sakamakon cutar sun haɗa da Taraba inda mutum 18 suka mutu, sai Ondo mai 17 da Edo mai 11 sai Bauchi da Ebonyi masu 6 kowanne da Gombe mai 5, sai Kogi mai 4 da kuma jihohin Nasarawa da Plateau masu uku jimilla.

Rahoton na NCDC ya kuma nuna cewa jihohin Ondo da Edo da Bauchi ne ke da kashi 75 cikin 100 na waɗanda aka tabbatar suna ɗauke da cutar.

Zazzaɓin Lassa dai cuta ce da ake kamuwa da ita daga mu’amala da wasu dabobbi dangin ɓeraye.

Comments (0)
Add Comment