Cutar Kwalara tayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu a jihar Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutum biyu sakamakon kwalara da ta zama annoba a Najeriya.Hukumomin lafiya na jihar sun ce sun dauki matakan gaggawa na dakile bazuwar cutar inda yanzu mutum 118 suka harbu a jihar.Dr Bishir Gambo Saulawa, kwamishinan lafiya na jihar ta Katsina ya shaida wa BBC cewa cikin matakan da suka dauka shi ne na samar da magungunan da suka kamata a matakin kananan hukumomi har da sinadarin tsaftace ruwa da suka rarraba.”Babban musabbabin kwalara shi ne ruwa, shi ne kuma ake kokari a rage.” in ji kwamshinan.A cewarsa, kananan hukumomin da aka yi asarar rayukan sune Dutsinma da kuma Katsina. Ya bayyana cewa cutar ta fi kamari a karamar hukumar Kusada inda a wajen kadai aka samu mutum 62 da suka kamu da cutar ta amai da gudawa.Kwamishinan ya ce babban aikin da ke gabansu a yanzu shi ne na dakile bazuwar cutar inda ya nuna cewa ana wayar da kan mutane game da muhimmancin tsaftace muhallansu domin kare kansu daga kamuwa da cutar ta amai da gudawa.

Comments (0)
Add Comment