Coronavirus Ta Kashe Mutum 300,000 A Brazil

Alkaluman da mahukunta suka fitar suna nuna cewa an samu mutuwar mutum fiye da dubu dari uku sakamakon cutar Coronavirus tun bayan da annobar ta bulla a kasar Brazil.

Hakan na nufin ita ce ke biye wa kasar Amurka mai mace-macen mutum akalla 545,000 tun daga bullar cutar kawo yanzu.

Ma’aikatar Kiwon Lafiyar kasar ta ce ya zuwa ranar Alhamis, mutum 300,685 ne suka riga mu gidan gaskiya ciki har da mutum 2,000 da suka mutu a sa’a 24 da ta gabata.

Wannan na zuwa ne yayin da shekaran jiya aka samu mutum 3,000 da suka mutu rana guda a Brazil sakamakon cutar Coronavirus, wanda shi ne mafi girman alkaluman mutanen da suka mutu rana guda da aka taba samu a kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Brazil wadda ita ce kasa mafi girma a yankin Latin, an samu mutum fiye da miliyan 12.2 da cutar ta harba kawo yanzu.

A halin yanzu, cibiyoyi masu bayar da kulawa ta musamman na ci gaba da fadi-tashi a jihohin kasar ba dare ba rana domin ceto rayukan wadanda ke da sauran kwanaki a doron kasa.

Ana zargin wannan mawuyacin hali da kasar ta tsinci kanta a yanzu na da nasaba da yadda tun da farko Shugaban Kasa Jail Bolsonaro, ya ki daukan matakin kulle sakamakon fargabar mummunan tasirin da hakan zai janyo ga tattalin arzikin kasar.

coronaCoronavirusCUTA
Comments (0)
Add Comment