Hukumar tsaron fararen hula, Civil Defense ta gargadi iyaye da a ko da yaushe suke sanya ido akan wadanda ‘ya’yansu ke mu’amala da su, musamman manya.
Kwamandan hukumar na jihar Jigawa, Mustapha Talba, ya fitar da gargadin lokacin da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa dake Dutse.
Yace gargadin ya zama tilas bayan ya lura da yadda iyaye suke watsi da ‘ya’yansu suke yawo a tituna neman abinci ko ilimi.
Sawaba Radio ta bayar da labarin cewa hukumar ta civil defense ta kama wani mutum mai shekaru 30 bisa zargin lalata wani almajiri dan shekara 13.
Mustapha Talba yayi bayanin cewa wanda ake zargin yayi amfani da halin da almajirin ke ciki inda yayi ta cin zarafinsa saboda yana bashi abinci.