Cire tallafin man fetur ya sa gwamnatina ta ninka kuɗaɗen da take bai wa jihohi – Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce cire tallafin man fetur ya sa gwamnatinsa ta ninka kuɗaɗen da take bai wa jihohi daga asusun tarayya sau uku.

Da yake magana yayin taron shugabannin jam’iyyarsu ta APC a Abuja jiya Talata da dare, Tinubu ya lissafa abubuwan da ya ce cire tallafin ya bai wa gwamnatinsa damar yi.

A lokuta da dama Sawaba radio ta rawaito yadda yan Najeriya suka fada kuncin rayuwa tun bayan cire tallafin man fetur a 2023.

Sai dai shugaban kasar ya tabbatar da cewa matsalolin da aka shiga laifin gwamnoni ne, domin basuyi abinda ya dace ba.

Comments (0)
Add Comment