China ta sanar da ƙara harajin kayayyakin Amurka zuwa kashi 125, daga kashi 84 da ta fara sanarwa a ranar Laraba da ta gabata.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen ke cigaba da tafka rikicin kasuwanci, inda ta ce yanzu aka fara.
Beijing ta ce idan Amurka ta ƙara ɗaga harajin, ita ma za ta ƙara ɗaga nata.
A cewarta, “ƙara harajin da Amurka ta yi mana ya saɓa da dokokin duniya da dokokin kasuwanci da cinikayya na duniya, ya kuma saɓa da tunani da hankali.”
“China ba za ta yi aminta da rainin hankali ba,” in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Lin Jian.
Tun da farko, ma’aikatar kasuwanci ta China ta bayyana ƙara harajin na Amurka a matsayin “kuskure a kan wani kuskuren,” lamarin da ta ce ba za ta lamunta ba.
A nasa ɓangaren kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya zargi China da rashim girmama ƙasarsa.