CBN ya musanta cewa ya fitar da sabbin takardun kudi na N5,000 da Naira 10,000

Babban bankin Najeriya, CBN, ya musanta wata takarda da ke cewa ya fitar da sabbin takardun kudi na naira 5,000 da naira 10,000.

Bankin ya bayyana takardar a matsayin “bogi” a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, yana mai jaddada cewa ya kamata jama’a su duba sahihancin labarai daga shafinsa na yanar gizo.

Takardar da ake yadawa a WhatsApp ta yi ikirarin cewa sabbin takardun kudi za su shiga kasuwa daga ranar 1 ga watan Mayu, tare da ambatar sunan wani mataimakin gwamnan CBN da ba a taba yi ba.

CBN ya yi kira ga jama’a da su guji yada labaran karya, yana mai tunatar da su cewa ta’ammuli da jabun kudin Najeriya babban laifi ne da ke da hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari.

Comments (0)
Add Comment