Majalissar kasar nan ta sake maidawa karamin ministan kwadago, ayyuka da aikin yi Mr Festus Keyamo martani, inda ta bayyana cewa ministan bai’san banbancin dake tsakanin kishin kasa da shugabanci ba.
Kafin hakan dai an bayyana cewa a ranar talata data gabata ne ministan yaki ya nemi afuwar majalissar saboda ya daga musu murya a zuwansa majalissar domin yin bayani kan shirin Gwamnatin tarayya na daukar mutane Dubu 774 a wani sabon tsarin da take kokarin farawa a fadin kasar nan.
- Majalisar Dokokin Legas ta sake zaɓen Obasa a matsayin kakakinta
- An yi garkuwa da wani ɗansanda a Abuja
- Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.22 ga dalibai 890
- Kungiyar NANS ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin Najeriya
- Kotun ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani
Inda daga bisani a ranar larabar data gabata majalissar ta bayyana kin amincewarta da tsarin saboda rashin yi musu cikakken bayani.
Yayin zantawa da manena labarai a jiya Juma’a shugaban kwamitin yada labarai na majalissar Mr Benjamin Kalu, ya bayyana cewa majalissar ta fiskanci cewa majallisar zartarwar na kokarin nuna musu cewa basu san aikin su ba.
Sannan ya kara da cewa samun Baraka tsakanin turakunan Gwamnatin guda 3 zai iya haifar da koma bawa wajan ci gaban al’umma. Sannan ya kara da cewa fahimtar junansu zai taimakawa kasar nan.