Buhari yayi alkawarin tabbatar da sahihin zabe a jihar Edo

Shugaban kasar yayi kira ga masu ruwa da tsaki a zaben da za a gudanar a gobe Asabar da su kauracewa abinda ya kira, ko a mutu ko ayi rai.

Matsayar Shugaba Buhari na kunshe cikin wata sanarwa wacce kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar.

Garba Shehu ya rawaito Buhari yana cewa ya jajirce matuka akan gudanar da zaben gaskiya da adalchi, amma jajircewarsa baza ta isa ba muddin masu aikin zaben suka ki kiyayewa da dokoki.

Shugaban kasar ya kara da cewa yana so yaga an dabbaka tsarin demokradiyya a kasarnan.

BuhariElection
Comments (0)
Add Comment