Buhari ya rantsar da Solomon Arase, a matsayin sabon shugaban hukumar ‘yansanda.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau ya rantsar da tsohon sufeto janar na ‘yansandan kasa, Solomon Arase, a matsayin sabon shugaban hukumar ‘yansanda.

Rantsuwar ta Solomon Arase wacce ta biyo bayan zaman ganawar majalisar zartarwa ta tarayya, na zuwa ne makonni biyu bayan majalisar dattawa ta tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar ‘yansanda.

Shugaba Buhari ya mika sunan Solomon Arase ga majalisar dattawa domin a tabbatar da shi kamar yadda yake bisa tanadin kundin tsarin mulki wanda aka yiwa gyara.

Solomon Arase, mai shekaru 65, wanda ya bar aiki a shekarar 2016, shine sufeto janar na ‘yansanda na 18, wanda ya rike mukamin daga watan Afrilun 2015 zuwa Yunin 2016.

Ya rike mukamai daban-daban da suka hada da shugaban sashen bincike da bayanan sirri na ‘yansanda. Shugaban kasar ya kuma rantsar da wakilai 5 na kwamitin gudanarwar kotun da’ar ma’aikata.

Comments (0)
Add Comment