Bola Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kamo maharan Dutsin-Ma da Kankara na jihar Katsina

Shugaba kasa Bola Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kamo maharan da suka kai hari a ƙananan hukumomin Dutsin-Ma da Kankara na jihar Katsina, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da tabbatar da an hukunta su.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman Ajuri Ngelale ya fitar a safiyar yau, yana mai kakkausar suka kan yawaitar hare-hare a ƙasar.

A yayin da ya bayyana sabbin hare-haren a matsayin munanan hare-hare, shugaban ya jaddada cewa za a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaron ‘yan kasa da kuma tarwatsa ‘yan ta’adda gaba daya, da sauran masu tayar da zaune tsaye da kuma baƙin ciki a kowane ɓangare na ƙasar.

Shugaban ya jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa, da gwamnati da kuma al’ummar jihar Katsina, tare da addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu.

Comments (0)
Add Comment