Bola Tinubu ya isa birnin Addis Ababa

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa birnin Addis Ababa, na ƙasar Ethiopia domin halartar zaman taro karo na 38 na shugabannin ƙasashen ƙungiyar Afirka ta AU.

Shugaban wanda ya sauka a birnin Addis Ababa a daren ranar Alhamis ya samu tarba daga mataimakin shugaban kula da harkokin ƙasar Ethiopian, Eshetu Legesse da ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar da kuma mai kula da ofishin jakadancin Najeriya da ke Ethiopian, Ambasada Nasir Aminu.

Daga baya Ambasada Tuggar ya yi wa shugaba Tinubu bayani kan taron da kuma wasu nasarorin diflomasiyya da ƙasar ta samu, zaman da ya kai har misalin ƙarfe 2:00 na tsakar daren jiya Juma’a.

Daga cikin nasarorin har da sake zaɓen Ambasada Bankole Adeoye a matsayin kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na AU.

Comments (0)
Add Comment