Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen da Gwamnatinsa ta yi ya zama dole wajen gyara tattalin arzikin Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi ya zama dole wajen gyara tattalin arzikin kasar, duk kuwa da kara wahalhalun da ake fuskanta da ke janyo fushin jama’a.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na a yayin bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya.

Tun bayan hawansa ƙaragar mulki a bara, Tinubu ya cire da tallafin man fetur wanda ya haddasa tashin gwauron zabin sufuri da farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi a fadin kasarnan. Dubban ‘yan Najeriya ne suka fito kan titunan Abuja da Legas a ranar Labara domin nuna adawa da yunwa da matsin tattalin arziki

Comments (0)
Add Comment