Gwamnatin tarayya tace, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinibu ya gina kasar nan kan tafarkin cigaba a cikin kwanaki 100 da yayi a Ofis.
Ministan yada labaraim Mohammed Idris ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya kan cikar shugaban kasa Tinubu kwanaki 100 a Ofis.
Mohammed Idris ya bukaci yan Najeriya da kungiyoyin kwadago, su cigaba da baiwa wannan gwamnati goyan baya tare da fuskantar ta.
Ministan ya bayyana cewa, tunda bayan da shugaba Tinubu ya shiga Ofis, gwamnatin sa ta kawo cigaba mai yawa ga kasar nan.
Ya kara da cewa, kasar nan na fama da tarun basussuka na ciki da wajen kasa, amma duk da haka shugaba Tinubu ya dauki matakin janye tallafin man fetur domin inganta tattalin arzikin kasar nan.
Ministan Yada labaran yace, kwanaki 100 na wannan gwamnati an yi kokarin inganta siyasar kasar nan da kuma kawo cigaba mai girman gaske.