Birtaniya Ta Daina Daukar Likitoci Da Masu Kula da Majinyata Daga Kasar Najeriya

Birtaniya ta sanya sunan Najeriya a cikin jerin ƙasashen da ba za ta rinƙa ɗaukan likitoci da masu kula da masu rauni daga ƙasar ba.
Birtaniyar ta ɗauki matakin ne bayan sabunta ƙa’idojinta na ɗaukan ma’aikata daga ƙasashen ƙetare.
A yanzu sunan Najeriya ya faɗa cikin waɗanda aka sanya wa launin ja ko ɗorawa, wanda yake fitowa daga Hukumar Lafiya ta Duniya.
Jerin ƙasashen wanda hakumar lafiya WHO ke sabuntawa bayan shekaru uku na nufin cewa ba za a ɗauki jami’an lafiya daga irin waɗannan ƙasashe ba.
Kasashen da matakin ya shafa sun hada da Afghanistan, Angola, Bangladesh, jamhuriyar Benin, Burkina Faso, Burundi, Cameroon, jamhuriyar Africa ta tsakiya, Chad, Comoros, Congo, jamhuriyar demkradiyyar Congo, Côte d’Ivoire, Djibouti, Equatorial Guinea, Eritrea, Ethiopia, Gabon, The Gambia, Ghana, Guinea, Guinea-Bissau, Haiti, Kiribati, Laos, da Lesotho da kuma sauran kasashe daga nahiyar afrika, gabas ta tsakiya dama Asiya.
Sai Dai Matakin Na Zuwa dai-dai lokacin da tarayyar najeriyar ta amince da dokar dake shirin talastawa likitoci share shekaru 5 suna aiki a najeriya kafin samun izinin fita zuwa kasashen ketare.

Comments (0)
Add Comment