Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da ake tsare da shi, Bello Bodejo ya musanta alakanta Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da halin da yake ciki a yanzu a hannun hukumomin tsaro.
Bodejo, wanda yayi magana ta bakin lauyansa, Mohammed Sherif a jiya Litinin, ya ce har yanzu bai yi wata magana ba a yayin da yake tsare a hannun hukumar leken asiri.
Ya mayar da martani ne ga wata kafar yada labarai da ta alakanta gwamnan da laifin da ake zarginsa da shi.
Sheriff ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ya sanyawa hannu kuma ya rabewa manema labarai a Abuja. Bodejo wanda ke fuskantar tuhume-tuhume uku na ta’addanci, an ruwaito a cikin sanarwar yana mai ikirarin cewa gwamnan ya matsa masa ya kafa kungiyar ‘ Zaman lafiya wadda tayi sanadiyar kama shi.