Bayanai na ci gaba da fitowa kan wata fashewa da ta janyo mutuwar wasu yara shida a karamar hukumar Gubio, da ke jihar Borno.
‘Yan sanda da jami’an yankin sun ce fashewar ta faru ne a wani gini da ke makarantar Islamiyya a ranar Asabar.
ASP Nahun Daso, kakakin rundunar yan sanda a jihar ta Borno ya shaida wa manema labarai cewa an tara wasu kayayyakin gwan-gwan da aka yi rashin sa’a wasu matasa da suka je wajen suka taru, a nan ne kuma aka samu abubuwan fashewa da suka tashi.
Rahotanni sun ce yaran kan tara ƙarafa da kuma sayar wa al’ummar yankin.
Duk da haramcin da aka yi kan sana’ar gwan-gwan, har yanzu ana cinikin lalatattun karafa a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula na masu tayar da ƙayar baya.
ASP Nahun ya ce suna wayar da kan mutane game da na’urorin fashewa tare da hana saye da sayar da kayan gwan-gwan.
Ya kuma kara da cewa rundunarsu za ta yi bincike a kan lamarin. Makonni biyu da suka gabata, wasu tubabbun ‘yan Boko Haram guda biyu sun halaka a wani bam da ‘yan ta’addan Boko Haram suka dasa a yankin Korede da ke karamar hukumar Damboa.