Barcelona zata kori Koeman, ta soma tuntubar Xavi kan yiwuwar maye gurbin sa

Rahotanni sun ce hukumar gudanarwar Barcelona ta soma tuntubar tsohon tauraronta Xavi Hernandez kan neman ya maye gurbin kocinta na yanzu Ronald Koeman, wanda shi ma tsohon dan wasan ta ne.

A makon nan ne dai fatan Barcelona na samun nasarar kulla yarjejeniya da Xavi a matsayin koci ya gamu da cikas, bayan da ya rattaba hannu kan tsawaita yarjejeniyar ta horas da tawagar kwallon kafar kasar Qatar da tsawon shekaru 2.

Sai dai wasu majiyoyi daga Barcelonan sun ce tuni shugaban kungiyar Juan Laporta ya nemi ganawa da tsohon kaftin din kungiyar ta Barca a cikin makon nan, domin tattunawa kan yi mata kome a matsayin mai horaswa.

XAVI
Comments (0)
Add Comment