Barazana ga masu shirin gudanar da zanga-zanga ba tsari ba ne na dimokuraɗiyya – Amnesty

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International ta yi gargaɗin cewa yin barazana ga masu shirin gudanar da zanga-zanga ba tsari ba ne na dimokuraɗiyya.

Yekuwar zanga-zangar da aka shirya gudanarwa daga daga ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa, ta samu karbuwa musamman a shafukan sada zumunta da kuma tsakanin wasu ‘yan kasa.

Hukumomi sun yi gargaɗi kan gudanar da zanga-zangar da za ta jefa ƙasar cikin tashin hankali tare da yin kwatanci da halin da ƙasashe kamar Kenya da Sudan da Libya ke ciki sakamakon yin bore.

A cewar Auwal Rafsanjani yi wa masu zanga-zangar barazana, zai gurgunta nasarorin Shugaba Bola Tinubu da ya samu a baya.

Sai dai duk da cewa gwamnatin tarayya ta ce ƴan ƙasar na da ƴancin yin zanga-zanga ta lumana, amma shugaban kungiyar CISLAC kuma babban jami’i a kungiyar Amnesty International, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce Dimukuradiyya ta ba ƴan ƙasa ƴancin fitowa su nuna damuwarsu.

Tun bayan da maudu’in da aka ƙirƙira mai taken “kawo ƙarshen rashin shugabanci nagari a kasa a shafukan sada zumunta, gwamnati da manyan jami’an gwamnati ke bayar da shawara ga matasan da suka ƙirƙiri maudu’in su ƙara haƙuri, suna masu bayyana fargabar cewa wasu na iya amfani da zanga-zangar su cutar da al’umma.

Comments (0)
Add Comment