Bankin CBN ya musanta karancin sabbin takardun kudaden Naira kamar yadda wasu ‘yan Najeriya ke zargi

Bankin CBN ya musanta karancin sabbin takardun kudaden Naira kamar yadda wasu ‘yan Najeriya ke zargi

Babban bankin kasa, CBN, ya musanta karancin sabbin takardun kudaden Naira kamar yadda wasu ‘yan Najeriya ke zargi.

Gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele, wanda ya samu wakilcin daraktan sashen kula da tsarin biyan kudi na bankin, Musa Jimoh, ya musanta zargin a wani taron manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato.

Godwin Emefiele ya shawarci ‘yan kasar da su ajiye kai tsaffin takardun kudinsu a kowane banki sannan su samu sabbi cikin gaggawa, yana mai jaddada cewa baza a taba karin wa’adin ranar 31 ga watan Janairu.

Gwamnan babban bankin na CBN ya bayyana cewa matakin sake fasalin takardun kudin ya nuna cewa babban bankin yana bisa turbar tsarin da duniya ke kai, inda ya kara da cewa ya kamata ake sake fasalin takardun kudin cikin shekaru 5.

Sai dai ya yi nadamar cewa Najeriya ta dauki shekaru 9 da yin irin wannan sauyin a karshe.

Gwamnan babban bankin na CBN ya ce matakin sake fasalin manyan takardun kudaden kasar nan wani aiki ne na kasa da ke da nufin magance matsalolin da suka shafi zagayawar kudade.

Comments (0)
Add Comment