Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce maganar da ake yaɗawa cewa Shugaban Najeriya Bola Tinubu na shirin canja mataimakinsa, Kashim Shettima a zaɓen 2027 ba gaskiya ba ce.
Daraktan watsa labarai na APC na ƙasa, Alhaji Bala Ibrahim ne ya bayyana hake a wata tattaunawarsa da jaridar Daily Trust, inda ya ce ko kaɗan babu wannan maganar.
“Raɗe-raɗi ne kawai. Maganganu ne na teburin mai shayi da bai kamata a ɗauka da muhimmanci ba. Don haka a yi watsi da maganar,” in ji shi.
“Ko da ma kuwa Shugaba Tinubu zai canja mataimaki, ba zai ɗauki matakin shi kaɗai ba. Dole sai an tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaju,”