Babbar Kwamashinan Burtaniya a Najeriya Catriona Wendy Laing Tace Ta Shiga Damuwa Domin Zata Bar Najeriya.

Babbar kwamashinan Burtaniya a najeriya Catriona Wendy Laing mai barin gado tace, ta shiga damuwa domin barin Najeriya, kasa mafi yawan al’uma a nahiyar Afrika.
Da take magana lokacin da ta ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari jiya a gidan gwamnati dake birnin tarayya Abuja, bayan aiki a najeriya na shekaru 4 da rabi, tace zata yi kewar Najeriya, musamman Wakoki, raye-raye da sauran al’adun Najeriya masu kayatarwa.
Ta taya shugaban kasa Muhammdu Buhari murna gama shekaru 8 a matsayi shugaban kasa, in da tace yayi aiki tukuru, ba dare, ba rana wajen hidinmtawa yan kasa.
Da yake mayar da martani shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Burtaniya ce kasar yan najeriya ta 2 ga mifi yawan yan najeriya, saboda huldar diplomasiyya mai karfi tsakanin kasashen 2.
Shugaba Buhari yace ya matsu yayi ritaya daga kujerar shugaban kasa ya koma garinsu Daura, dake jihar Katsina, bayan mika mulki a ranar 29 ga watan mayu mai zuwa, in yace zai yi nisa da birnin tarayya Abuja.

Comments (0)
Add Comment