Babbar kotun jihar Jigawa ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani mutum saboda aikata laifin kisan kai

Babbar kotun jihar Jigawa dake zamanta a Hadejia a jiya ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani mutum mai suna Magaji Hussaini (da aka fi sani da Lushe) bayan ta same shi da laifin aikata laifin kisan kai a karamar hukumar Kirikasamma ta jiharnan.

An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu bisa zarginsa da yin amfani da sanda wajen dukan wani mutum mai suna Muhammad Alhaji a wuyansa tare da raunata shi wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa a rugar Fulani ta Lamido Dadi da ke karamar hukumar Kirikasamma.

Lauyan mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu 6 tare da gabatar da hujjoji 3 wadanda suka kasance bayanan wanda ake kara da kuma hoton mamacin.

Alkalin kotun mai shari’a Honorabul Ado Yusuf, yayin da yake yanke hukuncin, ya ce kotun ta gamsu da hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar kuma ta tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba.

A saboda haka alkalin ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kisan kai wanda ke da hukuncin kisa a karkashin sashe na 221 na dokokin Penal Code na jihar Jigawa.

Comments (0)
Add Comment