Babangida ya bar abin alfaharin da ba za a taba mantawa da shi ba lokacin yakin basasar Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) murnar cika shekaru 82 a duniya.

Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce ya yi farin cikin murnar bikin tare da iyalan tsohon shugaban, abokansa, da kuma abokan huldar sa.

Ya ce Babangida ya bar abin alfaharin da ba za a taba mantawa da shi ba na kare martabar kasa a lokacin yakin basasar Najeriya. Ya yaba da gagarumar gudunmawar da Babangida yake bayarwa wajen ci gaban kasa.

Ya ce hakan ya hada da samar da jihohi da dama don karfafa tsarin tarayya, samar da ababen more rayuwa, da walwala ga masana’antar watsa labarai da sauran tsare-tsare a sassan kiwon lafiya da tsaro. Ya lura da irin gagarumin matsayi na Babangida wanda bayan shekaru 30 a kan mulki, ya ci gaba da kasancewa muryar hikima da nasiha ga yawancin shugabannin siyasa na ciki da wajen Najeriya.

Comments (0)
Add Comment