Ba zan rage yawan ministocina ba – Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya kare adadin yawan mutanen da ke cikin gwamnatinsa, wanda ya ƙunshi ministoci 48 da kuma wasu Masu Ba da Shawara na Musamman, inda ya ce hakan ya zama dole domin samar da ayyuka masu tasiri a ƙasar.

A cikin hirarsa ta farko da Shugaba Tinubu ya yi da manema labarai, wanda aka yi a daren jiya Litinin a gidansa da ke Legas, ya tabbatar da cewa, “Ba zai rage yawan ministocina ba.”

Ya bayyana cewa zaɓen ministocin yana da nasaba da inganci da buƙatun ƙasar.

Tinubu, ya jaddada cewa Nijeriya ƙasa ce mai girma tare da mutane sama da miliyan 200, kuma shugabancin irin wannan yawan al’umma na buƙatar shugabanni da dama. Ya ƙara da cewa yawan ministoci da masu ba da shawara suna da muhimmanci wajen gudanar da aikin ƙasar yadda ya kamata.

Comments (0)
Add Comment