Ba za mu goyi-bayan Isra’ila ta kai hari a cibiyoyin nukiliyar Iran ba – Biden

Shugaba Biden ya ce Amurka ba za ta goyi-bayan Isra’ila ta kai hari a cibiyoyin nukiliyar Iran ba, da sunan martani kan hare-haren makamai masu linzami da Tehran ta ƙaddamar kwanaki biyu da suka gabata.

A lokacin wani tsokaci da shugabannin manyan ƙasashen duniya na G7, Mista Biden ya buƙaci Isra’ila ta yi aiki da hankalinta.

Shugaban na Amurka na waɗannan kalamai ne bayan jakadan Isra’ila a MDD ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa za ta mayar da zazzafar martanin da Tehran ba ta taba tsammani ba.

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, shi ma ya aike da sakon gargaɗin cewa muddin Isra’ila ta tanka, to za ta sha mamakinsu.

Shugaba Masoud ya kuma shaida cewa tsaron yankin gabas ta tsakiya, tsaron Musulmai ne baki ɗaya, don haka ba za su raga ba, dominsu ba sa takalar yaƙi ko zubar da jini.

Comments (0)
Add Comment