Ba lallai Najeriya ta cike kujerun da ƙasar Saudiya ta ware mata ba a hajjin bana sakamakon samun ƙarancin masu biyan kuɗi a yayin da wa’adin da aka sanya na biyan kuɗi ke cika a yau 31.
Rahotanni na nuna cewa akwai yiwuwar samun gagarumin giɓi a kujerun da hukumomin Saudiyya suka ware wa ƙasar.
Ko a shekarar da ta gabata ma mutum 51,447 ne kawai suka biya cikin kujeru 95,000 da aka ware wa ƙasar.
Hukumar aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta sanya kuɗin kujerar hajjin 2025 a kan naira miliyan 8.78 ga jihohin kudancin ƙasar, yayin da na arewa maso gabashin ƙasar za su biya nai miliyan 8.32 , sai kuma naira miliyan 8.45 na jihohin arewa maso yammaci.
A Najeriya, daga shekarar 2019 zuwa yanzu, farashin kujerar aikin hajji ya ninka fiye da sau biyar inda a shekarar 2019 kuɗin ya kama naira miliyan 1.5, lamarin da ake ganin ba ya rasa nasaba da faɗuwar darajar naira idan aka kwatanta da dalar Amurka.