Matasan Jihar Katsina, karkashin kungiyoyin Fararen Hula na Arewacin Najeriya sun koka kan yadda ake samun hare-haren yan Bindiga, da Masu Garkuwa da Mutane domin neman kudin Fansa a Jihar Katsina, Inda suka nuna gazawar shugaban Buhari.
A cewarsu Kananan Hukumomin Batsari da Faskari na fuskantar hare-haren yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane domin kudin fansa, da kuma yiwa Mata Fyade wanda hakan ya shafi tattalin arzikin Al’ummomin kananan hukumomin, lamarin da suka bayyana cewa matukar ba’a magance matsalar ba zata shafi sassan jihar ta Katsina baki daya.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Mataimakin shugaban Kungiyar na Shiyar Arewa Maso Yamma Mista Jamilu Aliyu, ya rabawa manema labarai, bayan kammala zaman kungiyar wanda aka gudanar a Jihar Katsina kan hare-haren yan bindiga a jihar.
- Mutane da dama sun mutu bayan da wani jirgin sama ya yi hatsari a Kazakhstan
- Gwamnan Kebbi ya bada motocin shinkafa guda 3 don bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara
- Gwamnatin jihar Jigawa ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 a jihar
- Nijeriya ba ta cikin jerin ƙasashen da suka fi dogaro da lamuni daga IMF a Afirka
- Gwamnatin Tarayya ta wanke mutane 888 daga zargin ta’addanci
A cewarsa sace-sacen mutane domin neman kudin fansa ya zama ruwan Dare a Jihar, wanda ake gudanarwa a kullum.
Haka kuma kungiyar ta bukaci gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya binciki zarge-zargen da akeyi na Badakala da kudaden da gwamnati ta ware domin dakile hare-haren yan bindiga a Jihar.