Atiku Ya Kalubalanci Gwamnati Kan Tabarbarewar Tsaro a Najeriya

Har iya tsawon wane lokaci za mu ci gaba da kasancewa a cikin wannan hali na matsalar tsaro? In ji Atiku.

Tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya Atiku Abubakar, ya nuna takaicinsa kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a yankin arewacin kasar.

Atiku ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a karshen makon nan, bayan da rahotanni suka bayyana cewa an sace wasu daliban kwaleji a jihar Kaduna.

“Tambayar ita ce: har iya tsawon wane lokaci za mu kasance cikin wannan hali – matsalar tsaro?” Atiku ya rubuta Twitter.

Da yammacin ranar Juma’a hukumomin jihar ta Kaduna suka bayyana cewa an sace daliban kwalejin kula da gandun daji su 39 ciki har da mata 16.

Ko da yake rahotanni sun nuna cewa sojoji sun kubutar da wasu daga cikinsu.

“Tunaninmu da addu’o’inmu suna tare iyalan wadannan dalibai, yayin da nake kira da a yi amfani da duk abin da ake da shi wajen kubutar da su.” Atiku wanda ya yi wa babbar jam’iyyar adawa ta PDP takarar shugaban kasa a shekarar 2019 ya ce.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ake kaikaitar mata dalibai wajen yin garkuwa, wadanda ya ce su ne koma-baya wajen neman ilimi musamman a arewa.

“Hakan babban abin damuwa ne.” Ya ce.

Satar wadannan dalibai a jihar ta Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na zuwa ne kasa da mako biyu bayan da aka sako daliban matan makarantar sakandare ta Jengebe su 279 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Zamfara.

Matsalar garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a Najeriya musamman a arewa, inda ‘yan bindiga kan hari makarantun kwana don neman kudin fansa.

A ‘yan watannin baya-bayan kadai nan an sace mutane bila adadin a sassan arewacin kasar, wadanda suka hada da na daliban sakandaren Kankara na jihar katsina, sai na daliban Jangebe da ke jihar Zamfara.

Sauran sun hada da na fasinjar motar safa ta NSTA, da daliban makarantar Kagara duk a jihar ta Neja.

Matsalar garkuwa da mutane musamman dalibai, ta samo asali ne tun bayan satar ‘yan matan makarantar Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar wadanda mayakan Boko Haram sace a shekarar 2014, inda har yanzu ba a ga wasu daga cikinsu ba.

Buhari
Comments (0)
Add Comment