Tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo su rage kudaden da aka ware musu na tafiye-tafiyen su da kudaden Abinci su a kasafin kasa.
Ya ce manufar hakan shine domin a taimakin tattalin arzikin kasa daga kokarin durkushewar da yake kokarinyi saboda annobar Corona.
Atiku Abubakar, wanda shi ne dan takarar Jam’iyar PDP a kakar zaben da ta gudana na shekarar 2019, ya ce duk da cewa farashin man fetur ya karye a kasuwar Duniya kuma abinda gwamnatin tarayya take samu na bangaren da bana mai ba, ya gaza biyawa kasar bukata, amma abinda gwamnatin ta rage daga kudaden kasafin shine Biliyan 71 daga cikin Tiriliyon 10 da Biliyan 594 da ta ware.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinta sa na Twitter Atiku Abubakar, ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dakatar da kudurinta na gyara Majalisun wakilai akan kudi naira Biliyan 27.
Haka kuma ya ce kudaden da aka ware domin siyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa da sauran masu madafin Iko Motocin Alfarma, akwai bukatar suma a dakatar dasu, Inda ya bukaci a kyale Albashin ma’aikata, amma a rage albashin masu rike da madafun Iko.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ministar ma’aikatar kudi kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Sham’una Ahmad ta gabatarwa majalisar kasa cewa a sake rage Biliyan 71 da dubu 500 daga cikin kasafin kudin kasa, saboda dalilan tabarbarewar tattalin arzikin kasa.