Ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi alla-wadai da harin da aka kai ƙauyen Ƴargoje da ke jihar Katsina, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Harin da ‘yan bindiga suka kai, ya kuma haɗa da garkuwa da mata da kananan yara marasa galihu, lamarin da ya kara ta’azzara al’ummar yankin.
Da yake nuna alhininsa game da faruwar lamarin, Atiku ya yi ƙarin haske kan harin kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami’an tsaron da ke amsa kiran gaggawa a kauyukan Gidan Tofa da Dan Nakwabo wanda yayi sanadin mutuwar jami’an ‘yan sanda hudu da wasu ‘yan kungiyar sa ido na jihar Katsina guda biyu.
Atiku ya soki matakan da gwamnati ke dauka kan matsalar tsaro da ake fama da ita, inda ya nuna cewa ayyukan ‘yan fashi da ta’addanci sun zama ruwan dare gama gari.
Ya bayyana damuwarsa kan gazawar gwamnati da kuma rashin ɗaukar ƙwararan matakai, duk da gagarumin kasafin kudin shekara da ake warewa tsaro.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga gwamnati da ta kara daukar nauyinta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da muhimmanci.