Shugaban kasa Bola Tinubu ya samu goyon bayan al’ummar yankin Neja Delta a yakin da yake yi da satar man fetur domin inganta tattalin arzikin kasa.
Asari Dokubo, wani mai fafutukar yankin Neja Delta ne ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da ya ziyarci shugaban kasar jiya a Abuja.
Asari Dokubo ya ce wasu tsirarun ‘yan Najeriya ne da ‘yan kungiyarsu ke yin awon gaba da albarkatun man da ke yankin ba tare da kula da maslahar ‘yan kasa ba.
Ya ce masu fafutukar Neja-Delta za su tabbatar da cewa an yi amfani da dukiyar al’umma ta hanyar da ta dace domin amfanin yankin da al’ummarta.
Asari Dokubo ya ce ya tattauna sosai da shugaban kasar, inda ya ba da tabbacin cewa nan gaba kadan za a fitar da baragurbin da ke cikin tsarin domin tsaftace yankin Neja Delta.
Ya ce wasu ‘yan tsiraru mutane da kungiyoyi wadanda ba su da sha’awar ci gaban yankin Neja-Delta da ma Nijeriya baki daya baza su cigaba da cutar da kasarnan.