Sama da Babura masu kafa uku 200 ne dai kawo yanzu suke hannun jami’an yansada na jihar Yobe tun bayan da samari masu sana’ar tuka Adaidaita Sahu suka gudanar da wata zanga-zangar lumana a gaban babban ofishin yansanda na Damaturu don nuna rashin amincewarsu da yadda suka ce ake gallazawa rayuwarsu da dokoki iri-iri.
Masu tuka baburan dai sun fito kan tituna ne tare da iface-iface gami da kalaman nuna sun gaji da yadda yansanda ke yawaita kamasu.
Daga bisani ne kuma zanga-zangar ta rikide ta koma mai barazana da zaman lafiya, wasu suka fara cinna wuta tare da farfasa abubuwa mallakar gwamnati kamar fitilun kan hanya sabbi da aka saka.
Hakan ce kuma ta harzuka jami’an inda nan take suka mayar da martini ta hanyar harba hayaki mai sanya hawaye tare da harbi a cikin iska domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Ya zuwa yanzu dai babu rahotan rasa rayuwaka amma majiyar Sawaba FM ta tabbatar da cewa yansandan sun cafke Babura da dama
Masu sana’ar Adaidaita na cigaba da fuskantar barazana a jihohi da dama ciki har da Kano, inda shugaban hukumar KAROTA ya ce da yiwuwar ma su hana sana’ar gaba daya a jihar.