Ana zargin ‘Yan Najeriya masu arziki da daukar nauyin ‘Yan ta’adda a fannin hakar ma’adanai

Ministan ma’adanai Mista Dele Alake, ya zargi wasu daga cikin ‘Yan Najeriya masu arziki da daukar nauyin ‘Yan bindiga da ‘Yan ta’adda a fannin hakar ma’adanai.

Ministan ya fadi haka ne yayinda ya bayyana a gaban kwamitin kula da ma’adanai na Majalisar Dattawan domin kare kasafin kudin ma’aikatar sa.

Kazalika, Ministan ya zargi wasu daga cikin ‘Yan kasashen ketare da shiga harkokin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Yayi kira ga gwamantin tarayya data maida hankali dangane da makudaden kudade da take zubawa a fannin ma’adanai duk shekara.

Dele Alake, yace daga cikin Dala Bilyan 700 da gwamnatin tarayya ke sakawa a fannin hakar ma’danai, ba’a samun koda daya bisa uku na kudin.

Ministan ma’adanai yayi kira ga shugaban kwamitin ma’danai na majalisar dattawan da ya baiwa fannin goyan bayan daya dace, yana mai cewa hakan zai kawo sauyin a harkokin hakar ma’adana a Najeriya. Dele Alake, ya nemi kwamitin da yayi la’akari da kasafin kudin da aka warewa ma’aikatar hakar ma’adanai a cikin kasafin kudin shekarar 2024.

Comments (0)
Add Comment