Ana neman sama da Naira Triliyan ɗaya domin kammala shimfiɗa babban titin Abuja zuwa Kaduna

Ana neman sama da Naira Triliyan ɗaya domin kammala shimfiɗa babban titin Abuja zuwa Kaduna

Ministan ayyuka a Najeriya, Sanata David Umahi ya ce kamfanin gine-gine Julius Berger na neman sama da naira triliyan ɗaya domin kammala shimfiɗa babban titin Abuja zuwa Kaduna.

Da yake magana a wani taro da daraktocin ma’aikatar ayyukan a Abuja, babban birnin tarayya, ministan ya ce titin da farko an ware naira biliyan 165 wanda aka ƙara kuɗin zuwa naira biliyan 654.

Ya ce gwamnati ba ta da shirin biyan sabon farashin saboda rashin kuɗi.

Manema labarai sun ruwaito cewa an ba da kwangilar aikin a shekarar 2017 amma sai a 2018 aka soma aikin.

Yace Ya kamata yayi kammala titin cikin shekarar 2021 wanda ɗaya ne daga cikin ayyukan gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sai dai hakan bai samu ba har gwamnatin ta sauka a 2023 amma dai an kammala fiye da rabin aikin titin.

Comments (0)
Add Comment